YouTube ya cika shekaru goma da kafuwa

Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Dandalin YouTube yana da abokan huldatayya miliyan dubu

Dandalin nan na sadarwa ta Intanet na YouTube ya cika shekara goma cif-cif da kirkirowa ranar Alhamis.

Wasu daliban jami'a ne dai su uku 'yan kasar Amurka suka kafa dandalin a shekarar 2005.

Kuma shekara daya bayan kafa shi, kamfanin Google ya saye shi.

An dai yi imanin Shafin na YouTube na daya daga cikin shafuka ko dandali na Intanet mafi shahara da kuma farin-jini a duniya a halin yanzu.

Kuma kawo yanzu dandalin yana da abokan huldatayya kimanin miliyan dubu daya a fadin duniya.

Babban mahimmancin YouTube din shi ne ba wa mutane damar tallata ra'ayinsu ko haja ko kuma al'adu ga duniya ba tare da biyan ko anini ba.

Sai dai kuma kwararru na ganin cewa dandalin ya taimaka gaya wajen yada manufofin ta'addanci saboda yadda 'yan ta'addan ke yin amfani da shi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption YouTube yana ba wa mutane damar tallata kai ba tare da kudi ba

Bugu da kari, babbar illar da Youtube ya haifar ita ce na yadda matasa suka mayar da dandalin wata kafa ta kallon hotunan batsa.