Buhari zai gayyaci Obama, Cameron

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwamitin zai gayyanci Barack Obama da David Cameron domin halartar bikin rantsar da Buhari.

A Najeriya, kwamitin da shugaban kasar Goodluck Jonathan da shugaba mai jiran gwado, Janar Muhammadu Buhari suka kafa domin shirya bikin mika mulki ga gwamnati mai jiran gado ya ce zai gayyaci manyan shugabannin kasashen duniya da na Afrika -- cikinsu har da shugaban Amurka, Barack Obama da Firai Ministan Biritaniya, David Cameron -- domin halartar bikin.

Kwamitin, wanda Sakataren Tarayyar kasar, Cif Anyim Pius Anyim da tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Silva ke jagoranta ya ce ba kamar yadda aka saba a baya ba, a wannan karon ba za a gudanar da gagarumin biki ba.

Honourable Binta Masi Garba, mamba a kwamitin, kuma ta shaida wa BBC cewa sun dauki matakin kin yin biki mai yawa ne saboda kada su kashe kudade da yawa ganin mummunan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

A cewarta, za a gudanar da addu'oi a masallata da coci-coci domin rokon Allah ya yi wa gwamnatin Janar Buhari jagoranci.