Boko Haram ta kaiwa sojin Niger hari a Karamga

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Wannan ba shi bane karo na farko da mayakan Boko Haram ke kaiwa sojojin Niger hari

A Jamhuriyar Nijar, wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a tsibirin Karamga dake arewa maso gabashin Bosso, inda sojojin kasar da dama ke gudanar da ayyukansu.

Wasu rahotannin dai sun ce sojojin Nijar da dama sun halaka a harin, wanda ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram din sun kai ta hanyar yin amfani da kwalekwale masu inji.

Ma'aikatar tsaron Nijar ta tabbatar da aukuwar harin.

Sai dai babu cikkaken bayani dangane da yawan wadanda suka mutu a harin.

Wakilin BBC a Yamai ya ce wannan ba shi bane karo na farko da mayakan Boko Haram ke kai hari wannan tsibiri.

Masunta da makiyaya ne ke rayuwa a yankin.