Girgizar kasa ta hallaka mutane a Nepal

Aikin ceton girgizar kasa a Nepal Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Aikin ceton girgizar kasa a Nepal

'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane fiye da 970.

Akwai mutane da dama da suka sami raunuka yayinda wasu kuma ba a gano su ba.

Ana fargabar cewa adadin wadanda suka rasun ka iya karuwa.

Masu aikin ceto na cigaba da kokarin ceto wadanda suka tsira daga cikin buraguzan gine gine.

Girgizar kasar mai karfin maii 7.8 ta lalata gine gine da dama.

Gwamnatin Nepal din ta ayyana dokar ta baci ta kuma ce za ta nemi taimakon kasashen duniya.