Mutane biyu sun mutu a tarzomar Burundi

Akalla mutane biyu sun rasa rayukansu a wata arangama da ta barke tsakanin yan sanda da masu zanga zanga a Bujumbura babban birnin kasar Burundi.

Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi da kuma harbi da bindiga.

Masu zanga zangar sun zargi gwamnati da murda kundin tsarin mulki bayan sake tsayar da shugaba Pierre Nkurunziza domin neman tazarce a karo na uku.

Wakilin BBC a Bujumbura yace mutane da dama sun sami raunuka yayinda wasu kuma yan sanda suka yi awon gaba da su.

Wani mai zanga zangar yace jama'ar Burundi kan su a hade yake wajen adawa da shugaban kasar