Gadar sama ta kashe mutane 7 a Kano

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gwamnatin jihar ta Kano ta gina gadodji da dama.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce mutane bakwai ne suka mutu yayin da wani bangare na wata gadar masu tafiyar kafa da ake ginawa ya fadowa wata mota a Kano.

Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce bangaren gadar ya fado ne jim kadan bayan an dora shi.

Akasarin mutane da ke cikin motar dai mata ne da kananan yara.

Gwamnatin jihar ta Kano dai ta gina gadoji da dama a shekaru hudu da ta kkwashe tana yin mulki, kuma wannan shi ne karo na farko da gadar ta karye.

Sai dai a kwanakin baya wata gadar da gwamnatin tarayya ke ginawa a jihar ta karye, koda yake ba ta kashe kowa ba.