Ana ci gaba da aikin ceto a Nepal

Hakkin mallakar hoto AP

Kayan agaji sun fara isa Nepal yayida aikin ceto ke cigaba don taimakawa mutanen da girgizar kasa ta ritsa da su a Kathmandu.

Hakan nan kuma mutane goma sha bakwai sun mutu a tsaunin Mt Everest sakamakon zubar dusar kankara.

A waje guda kuma an sami tashin amo na girgizar kasa a Nepal kwana daya bayan girgizar kasar da ta hallaka mutane fiye da dubu biyu da dari uku.

Hari Kumar jami'in kula da kare aukuwar hadura masu nasaba da yanayin kasa a kudancin Asia yace gine gine a wuraren da basu dace ba na daga cikin dalilan da suka sa aka sami rushewar gine ginen musamman a Kathmandu a lokacin girgizar kasa