Ishaku ya lashe zaben Taraba

Hukumar zabe ta Najeriya ta yi shelar cewa dan takarar jam'iyyar PDP mai mulki, Mista Darius Dickson Ishaku, ya ci zaben gwamnan jihar Taraba.

Mista Ishaku ya kada 'yar takarar jam'iyyar adawa ta APC, Sanata Aisha Jummai Alhassan ce, amma ta yi watsi da sakamakon zaben tana cewa an tafka magudi.

A ranar Asabar ne aka kammala zaben a wasu yankuna jihar, bayan da aka soke na baya saboda zarge-zargen magudi da tarzoma a lokacin da aka yi zaben game-gari makwanni biyu da suka gabata.

A cewar hukumar zaben, a baki daya dai, Mista Ishaku ya samu jimlar kuri'u 369,318 yayin da Sanata Aisha Alhassan ta zo ta biyu da kuri'u 275,984.

Dangane da haka ne babban baturen zaben, Ferfesa Kyari Mohammed, ya bayyana Mista Ishakun a matsayin wanda aka zaba gwamnan jihar ta Taraba.

'Yan jam'iyyar PDP sun nuna jin dadinsu da sakamakon, inda daraktan yakin neman zabensu, Alhaji Abubakar Bawa, ya ce zaben ya yi kyau sosai.

To sai dai Sanata Aisha Alhassan da kuma jam'iyyarta APC sun yi watsi da sakamakon suna zargin cewa an tafka magudi.

Wakilinsu, Abubakar Gambo Umar, ya ki sa hannu a takardar sakamakon zaben.

Ya ce za su je kotu domin su kalubalanci sakamakon zaben.

Bayan sanar da sakamakon dai kome na tafiya lami lafiya a jihar ta Taraba, amma dai an baza jami'an tsaro birjit a kan tituna.

Karin bayani