Zanga-zanga a Burundi ta shiga rana ta uku

Hakkin mallakar hoto
Image caption Matasa a Burundi sun ce babu tazarce

An shiga rana ta uku ana zanga-zanga a Bujumbura babban birnin kasar Burundi domin adawa da yunkurin Shugaba Pierre Nkurunziza na tsayawa takara a karo na uku.

Mutane sun kona tayoyi a kan tituna inda suka saka shingaye a yayinda 'yan sanda suka harba musu barkonon tsohuwa domin tarwatsasu.

A karon farko zanga-zangar ta yadu zuwa wasu birane da ke wajen babban birnin kasar.

'Yan sanda sun hana daruruwan daliban jami'a shiga cikin garin Gitega domin yin zanga-zanga.

Majalisar dinkin duniya ta ce kusan 'yan Burundi dubu 25 sun fice daga cikin kasar a cikin makonni biyu bisa fargabar barkewar rikici a yayinda ake shirin gudanar da zabe a kasar.