'Yan Burundi na ci gaba da zanga-zanga

Image caption 'Yan sanda na daukar matakai a kan masu zanga-zanga

'Yan sanda a kasar Burundi sun fesa barkonon-tsohuwa a kan mutanen da suka shiga kwana na biyu suna zanga-zanga domin kin jinin takarar da Shugaba Pierre Nkurunziza zai tsaya a karo na uku.

Hukumomi sun tura sojojin kasar domin tunkarar masu zanga-zangar.

Zanga-zangar dai ta fi yin kamari a yankuna biyar na babban birnin kasar, Bujumbura, kuma an rufe kantuna da dama da ke tsakiyar birnin saboda zanga-zangar.

Tsohon shugaban kasar, Pierre Buyoya -- wanda ya tsoma baki har aka kawo karshen shekarun da aka kwashe ana rikice-rikice a kasar -- ya yi gargadin cewa Burundi za ta iya sake fadawa cikin yakin basasa.