Taraba: Aisha Alhassan za ta je kotu

Image caption Zaben Jihar Taraba ya bar baya da kura

'Yar takarar babbar jam'iyyar APC a jihar Taraba, Sanata Aisha Jummai Alhassan, ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan da hukumar zaben kasar ta ayyana abokin kararwarta Mr. Darius Ishaku a matsayin wanda ya yi nasara.

Sanata Aisha ta nace kan cewa ita ba ta sha kaye ba, inda ta yi zargin cewa an tafka magudi a kananan hukumomi da dama, kuma za ta kalubalanci sakamakon zaben a kotu.

Sanatar ta shaida wa BBC cewa za ta nufin kotu ne saboda ta yi imanin cewa ita ce ta lashe zaben amma aka murde aka bai wa dan jam'iyyar PDP.

Sai dai mutumin da hukumar zabe ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben, Mr. Darius Ishaku, ya yi watsi da wadannan zarge-zarge.

A baya, jihar ta Taraba ta sha fama da rikice-rikicen da ke da nasaba da addini da kuma kabilanci.