Fiye da mutane 3000 ne suka mutu a Nepal

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutanen da aka ceto daga girgizar kasa a Nepal.

Mahukuntan Nepal sun ce kawo yanzu fiye da mutane 3000 aka tabbatar sun mutu sakamakon bala'in girgizar kasa da ya afkawa kasar ranar Asabar.

Ana fargabar baraguzan gine-gine sun binne mutane da dama.

Mutanen da girgizar kasar ta lalata wa gidaje suna zama ne a tantuna da aka kakkafa a babban birnin kasar, Kathmandu.

Dubban mutane ne suka kwana a waje a rana ta biyu, inda suka kaurace wa gidajensu a yankin tsakiyar Nepal saboda fargabar da suka shiga bayan an sake samun kananan girgizar kasa ranar Lahadi.

Shugaban gidauniyar ba da agaji ta TEARfund, Ian Mclnnes, ya shaidawa BBC cewa mawuyaci ne adadin mutanen da suka mutu ya kai wanda aka samu a girgizar kasar Haiti a 2010, inda fiye da mutane dubu 100 suka mutu.

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce ana fuskantar karancin abinci da ruwan sha a kasar, sannan ana samun yawaitar daukewar lantarki.