Sturridge zai yi doguwar jinya - Rodger

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rodgers yana yiwa Sturridge huduba

Watakila dan kwallon Liverpool, Daniel Sturridge ba zai kara murza kwallo ba a kakar wasa ta bana, in ji kocinsa Brendan Rodgers.

Sturridge mai shekaru 25, ya soma jinya ne tun a ranar 8 ga watan Afrilu a wasan cin kofin FA tsakaninsu da Blackburn.

Rodgers ya ce "Bari mu gani ko zai dawo a kakar wasa ta bana ko kuma sai ban kamalla gasar."

A yanzu Liverpool na da sauran wasanni biyar a gasar Premier inda take kokarin tsallkewa zuwa gasar cin kofin zakarun Turai.

Manchester United ce a halin yanzu take mataki na hudu a kan teburin gasar Premier, inda ta bai wa Liverpool tazarar maki bakwai.