Kamfanin Apple ya samu riba mai yawa bana

Hakkin mallakar hoto Pasu Au Yeung FlickrCC
Image caption Kamfanin kera wayoyi da kwamfutocin Apple

Kamfanin kera wayoyi salula da kwamfutocin Apple ya ce ya sayar da wayoyin iPhone miliyan sittin da daya da dubu dari daya a watannin ukun farko na shekarar 2015.

Kamfanin ya ce cinikin da ya samu ya sa ribar sa ta karu da kashi 33 cikin dari idan aka kwatanta da ta bara.

Mahukuntan kamfanin na Apple suka ce sun samu ribar dala biliyan 13 da miliyan 600, yayin da kudin shigar kamfanin ya karu da kashi 27 cikin dari, wato dala biliyan 58.

Kasuwar wayoyin da kwamfutocin ta fi armashi a China da kashi 71cikin dari, inda kamfanin ya samu dala biliyan 16 da miliyan 800, kuma hakan ya haura kasuwar a Amurka a karon farko.

Sai dai kuma kwamfutocin iPad na kamfanin basu samu shiga sosai ba, inda dududu iPad miliyan 12 da 600 kamfanin ya sayar.

Hakan raguwa ce aka samu da kashi 23 cikin dari idan aka kwatanta da bara.