Boko Haram ta kashe sojojin Nijar 48

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Nijar tare da dakarun kasar

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce sojin kasar 48 ne suka mutu a lokacin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a kasar a makon jiya.

'Yan Boko Haram din sun kai hari ne a tsibirin Karamga a ranar Asabar, inda a nan ne sansanin sojin kasar yake, sai dai a lokacin ba a san adadin mutanen da suka mutu ba.

Sojin sun shaida wa BBC cewa dakarunsu 32 suka bata tun bayan da aka kai harin.

Rahotanni sun nuna cewar mayakan sun yi amfani ne da kimanin kwale-kwale 10 ne masu injuna suka je tsibirin a lokacin da suka kai harin.

Jamhuriyar Nijar dai ta sha fuskantar hare-haren Boko Haram tun lokacin da ta shiga cikin kasashen da suka daura aniyar yaki da 'yan kungiyar.

Kungiyar ta Boko Haram dai ta kashe fiye da mutane 15,000 yayin da sama da mutane miliyan uku suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren kungiyar.