An samu gawawakin 'yan jarida a Libya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan kungiyar IS a Libya

An samu gawawwakin wasu 'yan jarida guda biyar da ke aiki a wata tashar gidan Talabijin a Libya, watanni takwas bayan an sace su.

Wani jami'i a rundunar sojin Libyan ya zargi mayakan IS da kashe 'yan jaridar.

Ya ce an yi wa 'yan jaridar yankan rago-- hudu daga cikinsu 'yan Libya ne sai kuma daya dan- kasar Masar.

An ga gawawwakinsu ne a wajen birnin Bayda da ke gabashin kasar Libyan.

Sun bace ne a bara, bayan da suka dauko rahotan kaddamar da majalisar dokoki a Tobruk.

Suna kuma kan hanyarsu ne ta zuwa Benghazi a lokacin da suka ratsa ta birnin Derna wanda yake karkashin ikon mayakan IS masu ikrarin jihadi.