Nigeria:'Yan majalisa na cece-kuce a kan shugabanci

Hakkin mallakar hoto aliyu

A Najeriya wata sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin sabbin 'yan majalisar dokokin kasar da kuma tsofaffi 'yan majalisar game da maganar bayar da mukamai a majalisun dokokin kasar.

Sababbin zababbun 'yan majalisar na neman komai ya sauya a tsarin shugabancin majalisar -- wanda aka soma amfani da shi tun lokacin da aka soma demokaradiya a kasar-- inda suke so wasu daga cikinsu su zama shugabannin majalisar.

Sai dai a bangare guda, tsofaffin 'yan majalisar da aka sake zaba na ganin kamata ya yi a ba da fifiko ga tsawon lokacin da mutum ya kwashe a zauren Majalisar wajen jagorancin ta musamman idan aka yi la'akari da gogewar da suke da ita.

Wasu masana harkokin siyasa na ganin cewar wannan dambarwa ba sabon abu ba ne, "kuma gwagwarmaya ce ta mulki" in ji Dr Abubakar Kari, wani masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja da ke Najeriya.