Sojoji sun ceto mata 293 daga Sambisa

Boko Haram yara
Image caption Boko Haram ta sace mata da dama a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto 'yan mata 200 da kuma manyan mata guda 93 a lokacin da dakarunta suka kai samame a dajin Sambisa.

Kakakin rundunar sojin kasa na kasar, Kanal Sani Usman, ya ce binciken da suka yi ya nuna cewa babu 'yan matan Chibok a cikin matan da aka ceto.

Sai dai ya ce suna ci gaba da tantance matan da aka ceto domin gano inda suka fito.

Rundunar sojin Najeriyar ta kuma ce ta kame da kuma lalata wasu sansanoni na 'yan ta'addan da ke dajin Sambisa da suka hadar da sansanin Takumbere da Sasssa da ke yankin Alafa.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce an sace mata da 'yan mata da kananan yara kusan 2,000 tun daga farkon shekarar 2014 sakamakon rikicin Boko Haram.

Karin bayani