Saudiyya ta kama 'yan kungiyar IS 90

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Mayakan IS na ci gaba da kai hare-hare a yawancin kasashen da ke gabas ta tsakiya

Kasar Saudiyya ta ce ta kama mutane 99 da ta ke zargin 'yan kungiyar IS ne, mafi yawansu kuma 'yan ainihin kasar ne.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Saudiyya ya ce mutanen suna shirya kai hare-haren kunar bakin wake a wurare da dama da suka hada da ofishin jakadancin Amurka da ke Riyadh.

Kamfanin dillacin labaran ya ce mutanen sun kafa sansaninsu ne a wani kauye da ke tsakiyar yankin Qassim.

A bara ne kasar Saudiyyan ta sanar da aiwatar da tsattsauran hukunci ga duk wanda aka samu ya yi tafiya domin yin mubaya'a ga masu da'awar jihadi.

A shekarun baya ma Saudiyya ta yi kokarin dakile yunkurin tayar da hankalin da mayakan da ke da nasaba da Al-Qaeda suka so yi a kasar.