Mitsi-mitsin mutum- mutumi masu daukar abubuwa masu nauyi

An kirkiro da wasu mitsi-mitsin mutum-mutumi da suke iya daukar abubuwa da suka fi su nauyi sau 2000 a jami'ar Stanford.

Za a iya amfani da wadannan 'yan kananan mutum-mutumi a masana'antu ko kuma wuraren da ake gine gine

Wadanda suka kirkiro su, sun yi koyi ne da yadda wasu halittu su ke

Masana kimiyyar da suka hada da dalibai masu karatun digirin digirgir a jami'ar Stamford sun nuna wani dan karamin mutum-mutumi da yake iya daukar wani gilashi da ya dara kilogiram 1 a nauyi

Wani mutum mutumin kuma da yake da nauyin 20mg yana iya daukar abu mai nauyin 500mg