Buhari zai kaddamar da kwamitin karbar mulki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Janar Buhari ya ce zai yi aiki da mutanen da ke da mutunci.

Shugaban Najeriya mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari zai kaddamar da 'yan kwamitin da ya nada domin tsara yadda za a karbi mulki daga hannu shugaba Goodluck Jonathan.

A wani sako da mai bai wa shugaba mai jiran gadon shawara kan watsa labarai, Malam Garba Shehu ya aike wa da BBC, ta ce za a kaddamar da kwamitin ne da safiyar ranar Laraba.

Kazalika, sakon ya ce Janar Buhari zai gana da zababbun 'yan majalisar wakilan kasar gabanin kaddamar da kwamitin.

A makon jiya ne Janar Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin karkashin jagorancin fitaccen ma'aikacin gwamnati, Malam Ahmed Joda.

Sauran 'yan kwamitin ne su ne: Dr. Doyin Salami da Malam Adamu Adamu, wanda shi ne Sakataren kwamitin.

Haka kuma akwai Mr. Boss Mustapha, Malam Muhammad Hayatuddin, Alhaji Abubakar Malami (SAN), Gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, Chief John Oyegun, Mr. Festus Odimegwu, Dr. Ogbonnaya Onu, Mrs. Nike Aboderin, Mr. Wale Edun, Mrs. Bola Adesola, Barrister Solomon Dalong, Chief Audu Ogbeh, Sanata Hadi Sirika da kuma Birgediya Janar Lawal Jafaru Isa.