Buhari ya kaddamar da kwamitin karbar mulki

Image caption Janar Buhari mai jiran gado

Shugaban Nigeria mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari ya kaddamar da 'yan kwamitin da ya nada domin tsara yadda za a karbi mulki daga hannu shugaba Goodluck Jonathan.

A jawabinsa, Janar Buhari ya bukaci 'yan kwamitin su yi aiki tukuru kuma su tabbatar da bin gaskiya.

Kwamitin mai wakilai 18 na da Malam Ahmed Joda a matsayin shugaba a yayinda Malam Adamu Adamu ya ke matsayin sakataren kwamitin.

Wannan kwamitin ne kuma zai gana da na bangaren shugaba Jonathan mai barin gado domin ganin yadda za a mika mulki cikin lumana.

A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da sabon shugaban kasa, Janar Buhari a Nigeria a wani kasaitaccen buki a Abuja.