An daure wasu Misirawa a kan kona coci

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu magoya bayan Shugaba Mohammed Morsi, wanda aka tsige daga mulkin Masar.

Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa wasu masu kishin Islama 69 hukuncin daurin rai da rai bisa laifin kona wani coci.

An kona cocin ne yayin da wani rikici ya balle a garin Kerdasa da ke kusa da birnin Al-kahira a shekara ta 2013.

Rikicin --- wanda ya hada da wani hari da aka kai kan wani ofishin 'yan sanda, ya faru ne sa'o'i kadan bayan da dakarun tsaro suka tarwatsa magoya bayan hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi daga manyan sansani biyu.

An kashe daruruwan masu zanga-zanga a wadannan lokutan.