''Kwamitin Buhari na wuce gona da iri''

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption A ranar 29 ga watan Mayu ne Buhari zai karbi mulki daga Jonathan

Gwamnatin Nigeria mai barin gado ta zargi kwamitin tsara yadda za a karbi mulki na bangaren Janar Buhari da wuce gona da iri.

Ministan tsare tsare na kasar Abubakar Sulaiman, ne ya yi zargin bayan taron majalisar zartarwar kasar ranar Laraba.

Ministan ya ce, kwamitin karbar mulkin na yunkurin azalzalar gwamnati kan neman bayanai.

Gwamnatin ta zargi kwamitin na Buhari da daukar kansa tamkar wata gwamnati da aka riga aka rantsar.

A martanin da ya mayar game da zargin Barrister Solomon Dalong, dan kwamitin karbar mulkin na Buhari, ya yi watsi da zargin.

Barrister Dalong y shaida wa BBC cewa, suna bukatar cikakkun bayanai ne kawai daga gwamnatin mai barin kado, kuma mulki ba abu ne da za a mika musu ba a kudundune kawai.

A ranar Laraba ne shugaban kasar mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari, ya kaddamar da kwamitin nasa mai wakilai 19 a karkashin jagorancin Ahmed Joda, tsohon babban sakatare a gwamnatin tarayya.