An yi garan bawul a masarautar Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarki Salman ya shigo da wani sabon abu a masarautar Saudiyyan, inda ya nada mutumin da ba jinin masarautar ba ne a kan muhimmin mukami.

Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud ya gudanar da garanbawul ga wasu muhimman mukaman gwamnati, inda ya saba al'adar gidan Sarautar a wajen rabon mukamai.

Wasu na yi wa wannan mataki kallon take-take na janye kansa daga makusantan Marigayi Sarki Abdallah.

Sarki Salman ya sallami dan-uwansa wanda suke uwa daya, Muqrin, daga mukamin Yarima mai jiran gado.

Kazalika ya nada dan gidan dan-uwansa, Mohammed Bin Nayef, a mukamin na Yarima mai jiran gado.

Ya kuma nada dansa Mohammed Bin Salman a matsayin mataimakin Yarima mai jiran gado.

Sarkin na Saudiyya ya amince da murabus din ministan harkokin waje mafi jimawa a kan mukamin, Yarima Saud Al Faisal, inda ya nada jakadan Saudiyyan a Amurka, Adil Al -Jubair, wanda kuma ba jinin sarauta ba ne.