Ana bikin shekaru 40 da gama yaki a Vietnam

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wani sashe na lokacin yakin na Vietnam

A Vietnam, ana wani gagarumin faretin soji a titunan birnin Ho Chi Minh don bukukuwan cika shekaru 40 da kawo karshen yakin kasar.

A rana irin ta yau ne dai a shekarar 1975, dakarun 'yan kwaminis suka kwace birnin, wanda a wancan lokacin ake kira Saigon, babban birnin kasar Vietnam ta Kudu.

Nasarar da Vietnam ta Arewa ta yi ce ta kawo karshen zazzafan rikicin yakin cacar bakan da ya haddasa mutuwar 'yan kasar ta Vietnam akalla miliyan uku, da sojojin Amurka dubu hamsin da takwas.

Wannan nasara ce kuma ta assasa hadewar kudancin da arewaci a matsayin kasa daya.