An rufe jami'a a Burundi

Image caption Jami'an gwamnati su fitar da dalibai daga dakunan kwanansu a jami'ar Bujumbura

Hukumomi a Burundi sun rufe jami'ar da ke Bujumbura, babban birnin kasar, bayan da aka shafe kwanaki ana zanga-zangar adawa da shugaba Pierre Nkurunziza.

Jami'an gwamnati sun shiga bangaren kwanan dalibai inda suka umarci daliban su kwashe jakunkunansu su bar makarantar.

A hannu guda kuma ana ci gaba da zanga-zangar a babban birnin a kan shirin da shugaban kasar yake yi na tazarce a karo na uku.

Manyan jami'an diplomasiyya na Amurka suna tattauna wa da gwamnatin Burundi domin kokarin shawo kan lamarin.

Mutane biyar ne suka mutu tun farkon fara zanga-zangar a karshen makon jiya.