Libya: Cibiyar safarar mutane ta duniya

Hakkin mallakar hoto Almoustapha Alhacen
Image caption Daya daga cikin irin motocin da ake safarar 'yan ci rani a ciki

A wurin wani binciken ababen hawa a wajen garin Misrata na Libya, masu gadin kan iyaka sun tsaida wata motar daukar kaya makare da busasshiyar ciyawa suka hau bincikarta, sai ga sirrin boye ya fito fili.

Abin mamaki! Ashe motar dauke take da yara da manya maza da mata 'yan ci-rani kimanin 50 a cunkushe a ciki.

Haka ake safararsu cikin mawuyacin hali a tsallake da su hamada.

Kwanansu biyu a cikin motar nan ba ci ba sha.

Image caption Abdul Rahim ya ce ya ga wulakanci kala-kala

Abdul Rahim--wanda ya taba samun kansa cikin irin wannan hali ya ce ya zaci mutuwa zai yi.

Tun tuni aka kai shi gidan kaso a Libya.

Ya shaida wa BBC cewa "Sai da na biya kimanin naira 500,000 don kawai a yi safara ta. Haka aka dinga tafiyar damu kamar kaya."

'Kazamin Kudi'

Masu fasa kwabrin basu cika son tambayoyi ba a kan harkarsu, bayan da wakilin BBC ya shafe makonni yana neman wanda zai yi hira da shi, a karshe da kyar ya samu wani ya amince da sharadin za a boye sunansa.

Ya yi kazamin kudi a wannan harka ta safarar mutane.

Ya ce kudin da ake samu ba kadan bane, "kwale-kwalen kamun kifi na kimanin naira miliyan shida za a iya sayar da shi kimanin naira miliyan 30. Kudi na fitar hankali."

Ya kara da cewa "Kwale-kwalen daga Misra ake sayo su kuma basu da inganci sai mu loda musu mutane 90 ko 100, wasu su kai labari wasu kuma su mutu."

Image caption Yadda daruruwan 'yan ci rani ke yin dandazo yayin da suke jira a loda su cikin kwale-kwale

Wakilin BBC ya kuma tambaye shi batun wadanda ke nutse wa a cikin teku.

Shi kuma sai ya ce "Ai mu kan gaya wa 'yan gudun hijira komai kafin su shiga kwale-kwalen, kuma kowanne da kudinsa, iya kudinka iya shagalinka."

Ga dukkan alamu mutane da dama na cin abinci ta harkar safarar mutane.

'Gawawwaki'

Ramadan Rajab shi ne mai kula da wajen ajiyar gawawwaki na birnin kimanin shekaru 15, ya ce a yanzu haka ba iya tantance kanshi ko wari tun bayan fara aikinsa a wajen.

Amma warin da wajen ya ke yi ya wuce misali.

Image caption Ramadan Rajab ya ce a yanzu haka ba ya iya jin kanshi ko wari tun bayan fara aikinsa a wajen.

Babu isasshen wajen da za a ajiye gawawwakin domin haka a waje ake shanya wasu cikin zafin rana.

Ramadan ya ce "Ko a makon da ya gabata mun binne fiye da gawawwaki 20 da muka dauko daga teku, wani lokacin ya kan dauke mu wata guda kafin mu gama tattaro dukkan gawawwakin. Yawan mutanen da ke mutuwa karuwa ya ke koda yaushe."

Wani lokaci masu fasa kwabrin suna guduwa su bar 'yan gudun hijirar a tsakiyar hamada. Sai kawai su ce musu "ku bi wadannan tarakunan lantarkin za ku tarar da gari."

Da yawa daga cikin 'yan ci-ranin basu kai labari ba.

Duk da cewa 'yan ci ranin talakawa ne, yawansu na sa wa wasu lokutan su sami abin-hannu in suka sami hayewa wannan siradi.

Duk da wadannan mace-mace, wasu a kullum sai sun zo domin a yi safararsu.

Wannan harka dai na tattare da sa'a ga wasu amma kuma tana cike da tarin hadura.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Duk da wadannan mace-mace, wasu a kullum sai sun zo domin a yi safararsu.

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a baya-bayan nan ya kimanta cewa harkar za ta iya kawo wa wasu kudi har pam miliyan 100 a shekara.