'Mai rabon ganin badi a Nepal'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An wuce da yaron asibiti bayan da aka ciro shi daga cikin baraguzan

Masu aikin ceto a Kathmandu babban birnin Nepal, sun ciro wani yaro mai shekara 15 daga cikin baraguzan gini kusan kwanaki biyar bayan mummunar girgizar kasar da ta auku a birnin.

Yaron dai ya rayu ne da taimakon iskar da yake shaka wacce ke shiga ta tsakanin tulin baraguzan da ya rufe shi.

Jami'ai sun ce izuwa yanzu mutane fiye da 5500 ne aka hakikance sun rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar wacce ta auku a ranar Asabar.

Kauyukan da ke kusa da inda girgizar kasar ta fi kamari na fama da karancin abinci da ruwan sha da matsugunai, kuma a cewar Majalisar Dinkin Duniya za a yi tafiyar kwanaki biyar da kafa kafin a kai garesu.

Sufeto Rajan Raj Upreti jami'i ne a rundunar 'yan sanda ta Kathmandu, ya kuma ce "Muna fama da karancin wutar lantarki, shi ya sa ba ma iya amfani da manyan na'urorin tono ko na yankan karfe, sannan ga damina da muke fama da ita."

Majalisar ta Dinkin duniya ta nemi taimakon dala miliyan 415 domin taimaka wa kasar ta Nepal a watanni uku masu zuwa.