An kara ceto wasu mata daga Sambisa

Sojojin Najeriya
Image caption Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta lalata sansanoni tara na Boko Haram ranar Laraba

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce ta kubutar da wadansu karin mata da yara daga Dajin Sambisa da yammacin jiya Laraba.

Rundunar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mukaddashin kakakinta, Kanar Sani Usman Kuka-Sheka, ko da yake ba ta bayyana adadin mata da yaran ba, ba ta kum ayi karin bayani a kansu ba.

Sai dai sanarwar ta ce abin takaici mata guda ta rasa ranta yayin da wasu matan suka yi raunin sakamakon harbinsu da bindiga da aka yi.

A cewar rundunar sojin kasar ta Najeriya, tuni aka kwashe matan zuwa wani amintaccen wuri, inda za a kula da su.

Sanarwar ta ce an ceto wadannan mata da yara ne a ci gaba da yunkurin da sojojin kasar ke yi na kakkabe sansanonin 'yan kungiyar Boko Haram daga Dajin na Sambisa.

A kan haka ne, inji sanarwar, soja daya ya rasa ransa, wasu hudu kuma suka ji rauni.

Rundunar ta kara da cewa dakarunta sun kashe kwamandoji da mayakan kungiyar Boko Haram din da dama sannan suka lalata motoci biyu masu sulke, da wasu motocin biyu masu dauke da bindigogin kakkabo jiragen sama, da motoci kirar Hilux da dama.

Ranar Talata ne dai Hedkwatar Tsaro ta Najeriyar ta ba da rahoton kubutar da mata 93 da 'yan mata 200 daga Dajin na Sambisa. Sai dai kuma hukumomin tsaron sun ce ba ko daya daga cikin 'yan matan nan da aka sace daga makarantar Chibok shekara guda da ta gabata.

Karin bayani