Karancin mai ya kawo tsaikon taimakon abinci a Yemen

Hakkin mallakar hoto AFP

Shirin samar da abincin na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma ce yana da isasaun kayan abinci ga mutane kusan miliyan daya da rabi har na tsawon wata guda, amma kuma ba za su iya kaiwa ga wadanda ke da bukatar ba.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce babban asibitin dake Sanaa babban birnin kasar na fsukantar karancin man petur na injinan bayar da hasken wutar lantarki.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga a basu damar kai kayan agajin zuwa tashar jiragen ruwa ta birnin Aden na kasar ta Yemen, amma---amma kuma nan ne inda ake fafatawa tsakanin 'yan tawayen Houthi da mayaka masu goyon bayan gwamnati.

Yayinda ake cigaba da gwabza fada a birnin Aden birni mai tashar jiragen ruwa na kasar Yemen, ana nuna damuwa kan halin da fararen hula ke ciki a can.