Fararen hula na cikin tasku a Yemen

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fada ya tsananta tsakanin mayakan sa kai masu goyon bayan gwamnati da 'yan tawayen Houthi.

Ana ci gaba da nuna damuwa kan halin da fararen hula suke ciki a birnin Aden na kasar Yemen, yayin da yaki fada ke kara kamari.

Kungiyar bayar da agaji ta likitoci wato Doctors Without Boarders, ta ce titunan garin na da matukar hadari ta yadda suke yi wa mutane wahalar bi domin samun zuwa asibiti.

Ana kai hari har a kan motocin daukar marasa lafiya da harbe-harbe ta ko ina da kuma tare hanyoyi.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin 'yan tawayen Houthi da mayakan sa kai masu goyon bayan gwamnati a kusa da filin jiragen sama.

Ya kuma ce "Babu isasshen abinci da magunguna da sauran abubuwan more rayuwa a wannan yankin."

Mutumin ya bayyana cewa al'amarin ya sa mutane cikin matsanancin hali ta yadda har suna barin garin.