Zuma ya gana da Jonathan kan kyamar baki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kashe mutane bakwai a lokacin hargitsin

Shugaba Jacob Zuma na Afrika ta Kudu ya kira shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ta wayar tarho domin tattauna batutuwan da ke faruwa a cikin kasar musamman na nuna kin jin 'yan ci-rani.

Shugabannin biyu a tattaunawar sun sha alwashin ci gaba da hada gwiwa tsakanin kasashensu domin ci gaba al'ummominsu.

Shugaban Jonathan ya kuma jadadda goyon bayansa ga gwamnatin Afrika ta Kudu a kokarinta na dakile hare-haren da ake kai wa 'yan ci-rani a wasu biranen kasar kamarsu Durban da Johannesburg.

Kasashen Afrika da dama sun caccaki mahukunta a Afrika ta Kudu game da yadda ta kasa kare 'yan ci-rani a cikin kasarta.

Mutane bakwai ne aka kashe a hare-haren da aka kaiwa 'yan ci-ranin a Afrika ta Kudu a cikin wannan watan.