Nijar ta bukaci mutane su fice daga tafkin Chadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Nijar na cikin sojojin da ke yaki da Boko Haram

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun bukaci mutanen da ke zaune a tsibiran da ke kusa da tafkin Chadi su fice daga wurin domin kauce wa hare-haren 'yan Boko Haram.

Hakan na zuwa ne bayan da 'yan Boko Haram a karshen makon da ya wuce suka hallaka mutane kusan 74.

Wata sanarwa daga gwamnan Diffa ta ce kiran ya zama wajibi domin kare lafiyar al'ummar da ke zaune a tsibiran.

Sanarwar ta ce daga nan zuwa ranar 4 ga watan Mayu, ya kamata al'umomin da ke tsibiran su ketara tudun mun tsira.

Jihar Diffa da ke kudu maso gabashin Nijar na kan iyakar da yankin arewa maso gabashin Nigeria mai fama da rikicin Boko Haram.

An ambato ministan harkokin cikin gidan Nijar, Hassoumi Massaoudou yana cewa sun kashe 'yan ta'adda 156 a lokacin harin da 'yan Boko Haram suka kai wa dakarun kasar a tsibirin Karamga.