Nigeria: Sojoji sun kara ceto mata da yara

Hakkin mallakar hoto
Image caption Manjo Janar Chris Olukolade darektan hulda da jama'a na hedikwatar tsaron Nigeria

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce, dakarunta sun sake ceto wasu tarin mata da yara har 234 daga sansanonin mayakan kungiyar Boko Haram, a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

Hukumomin sojin sun ce, sun yi wannan nasara ne a farmakin da suka kai ranar Alhamis a yankunan Kawuri da Konduga na makeken dajin.

Tun da farko a cikin makon nan rundunar sojin ta ceto wasu matan da yaradaruruwa daga sansanonin 'yan Boko Haram din a wannan daji na Sambisa.

Mukaddashin darektan hulda da jama'a na hedikwatar tsaron Najeriya Kanar Sani Usman Kuka-Sheka, ya gaya wa BBC cewa, ana kokarin tantance mutanen domin ko iyalan mayakan ne ko kuma wadanda suka yi garkuwa da su ne.

Kanar din ya kuma ce dakarunsu ba wai suna son kashe kowa ba ne, yana mai cewa suna maraba da duk wanda zai ajiye makaminsa ya mika ya wuya cikin 'yan Boko Haram din.