An kashe mutane a samamen sojin Nigeria

Hakkin mallakar hoto nigeria defence forces

Rahotanni daga Najeriya sun ce sojoji sun kai samame a wasu kauyuka na karamar hukumar Wase da ke kudancin jihar Filato da kuma wani kauye a jihar Taraba.

Mazauna yankin sun ce akalla mutane 10 ne suka rasu baya ga gidaje da dama da aka kona a sanadin samamen.

To sai dai rundunar tsaro ta musamman da ke aikin kiyaye zaman lafiya a jihar Filato ta ce dakarunta sun kai samamen ne domin yaki da 'yan bindiga da suka addabi yankin.

Ya ce hakan ya biyo bayan hare-haren 'yan bindigar, wadanda suka halaka sojoji da farar hula a jihohin Filaton da Taraba..

Rahotannni dai sun ce ranar Asabar ne aka ga sojojin cikin damara sun far wa kauyukan, wadanda galibin mazaunansu 'yan kabilar Taroh ne.

Mista Jangle Lohbut, shugaban 'yan kabilar Taroh a karamar hukumar ta Wase, ya ce kauyuka ukku ne samamen ya shafa a karamar hukumar Wase, sai kauye daya a cikin jihar Taraba mai makwobtaka.

To sai dai kakakin rundunar tsaro ta musamman mai aikin kiyaye zaman lafiya a jihar ta Filato, Kaftin Ikedichi Iweha, ya musanta cewa sojoji sun kai hari kan farar hula.

Ya ce sojoji sun kaddamar da samamen ne kan wadanda 'ya kira mayakan sa-kai masu dauke da makamai wadanda kan kai hare-hare har a cikin jihar Taraba, inda a hari baya-bayan nan a wannan mako suka kashe mutane da dama ciki har da sojoji shidda.

Karin bayani