Bam ya kashe mutane 13 a Bagadaza

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hare haren bam na mota ya zama ruwan dare a Iraki

Wani harin bam da aka kai a Bagadaza, babban birni kasar Iraki, ya hallaka mutane akalla goma sha uku.

Wasu mutanen fiye da talatin ne kuma suka jikkata lokacin da bam din, wanda aka dana a wata mota, ya tashi a kusa da wani shahararren gidan abinci.

Harin, wanda aka kai a gundumar Karrada inda 'yan Shi'a suka fi yawa, daya ne daga cikin hare-haren da suka yi muni a bana a birnin na Bagadaza.