Nepal: Ana debe kauna da samun masu rai

Image caption Dubban mutane ne ke aikin ceto a kasar Nepal bayan girgizar kasar makon jiya

Fatan sake samun masu nisan kwana a cikin baraguzan da mummunar girgizar kasa ta haddasa a Nepal mako guda da ya gabata na dusashewa.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gida, Laxmi Prasad Dhakal, ya ce ba ya zaton akwai yiwuwar samun wasu karin mutane da ransu a karkashin baraguzan.

A cewarsa adadin mutanen da suka rasa rayukansu yanzu ya haura dubu shida da dari shida.

Har yanzu ba a san inda dubban mutane suke ba, ciki har da mutane dubu daya daga nahiyar Turai wadanda suka yi batan dabo.

Jiragen sama masu saukar ungulu akalla ashirin ne ke aikin kai agaji a kauyukan kasar da ke yankin arewacin tsaunin Himalayas.

Karin bayani