An haifi Gimbiya a Birtaniya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Duchess ta Cambridge, matar Yarima William -- wanda shine na biyu a jiran gadon sarautar Birtaniya -- ta haifi 'ya mace a ranar Asabar din nan.

Jama'a masu fatan alheri tare da 'yan jaridu sun yi dafifi a wajen asibitin St Mary's a London inda wani mai shela na gidan sarautar ya bada sanarwar haihuwar.

Jama'a sun barke da shewa da murna yayin da suka ji shelar.

Wata sanarwa da aka fitar a hukumance daga iyalin gidan sarautar ta ce uwar da kuma jaririyar suna cikin koshin lafiya kuma Yarima William na wurin lokacin da aka hafi 'yar tasa.

Jaririyar wacce za'a rika kira da suna Gimbiyar Cambridge a hukumance za ta kasance ta hudu a layin masu jiran gadon sarautar Ingila.

Yerima William dai ya auri Kate ne a watan Aprilun shekara ta 2011.

Sun kuma haifi dansu na farko, Yerima George, a cikin watan Julin shekara ta 2013.

Karin bayani