'Mun sha azaba a hannun 'yan Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto AFP

Wasu daga cikin mata da yaran da sojojin Najeriya suka ceto daga hannun 'yan Boko Haram a dajin Sambisa sun shaida wa BBC cewa sun sha matukar azaba.

Dakarun Najeriyar dai sun ceto daruruwan mata da yara kanana a dajin na Sambisa da ke jihar Borno a arewa-maso gabacin kasar.

Sun kuma kai 275 daga cikinsu a wani sansani kula da 'yan gudun hijira da ke Yola, jihar Adamawa.

Wata mata 'yar shekaru 27 da haihuwa ta ce 'yan Boko Haram sun kama ta ne tare da mijinta a kasuwa.

Ta ce: "Sun dauke ni tare da shi, suka kaimu cikin daji, suka yanka shi.

"Suka ce dama sun dauke ni, domin in auri babbansu. Amma ashe ina da cikin arne. Suka ce tunda arne ya yi mani ciki, to, sun kashe shi.

"Suka ce idan kin haihu da sati daya zamu aure ki. Na haihu da dare, da safe aka zo aka cece mu."

Wasu matan ma sun bayyana cewa mayakan Boko Haram sun kashe mazajensu da yara maza a gabansu.

Sun kuma tilasta ma wasunsu suka aure su.

Sun ce mayakan sun tsare su, suna basu abinci sau daya a rana -- garin masara -- abin da ya jawo wasunsu suka mutu, wasu kuma suka kamu da cututtuka.

Karin bayani