Faransa ta ja kunnen sojinta kan lalata

Ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian

Jean-Yves Le Drian yace duk wani sojan Faransa da ya san yana da hannu a badakalar lalata da kananan yara a Jamhuriyar tsakiyar Afirka ya fito tun wuri ya baiyana kan sa.

Yace ya yi matukar bakin ciki lokacin da ya sami labarin zargin cewa sojojin Faransa da aka tura Jamhuriyar tsakiyar Afirka kafin kafa rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya sun yi lalata da kananan yaran dake jin yunwa domin basu abinci.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta musanta zargin cewa ta yi rufa - rufa akan cin zarafin wanda ya fito fili bayan da aka tsegunta rahoton binciken cikin gida na Majalisar Dinkin Duniyar.