Sojin Italiya sun ceto 'yan ci-rani 3500

Hakkin mallakar hoto

Dakarun Italiya masu tsaron gabar ruwa sun ce sun ceto fiye da 'yan ci-rani 3,500 makare a kananan jiragen ruwa suna kokarin ketara Tekun Baharum daga nahiyar Afirka a sa'o'i ashirin da hudu da suka wuce.

Wakilin BBC ya ce wadanda aka ceto a yunkurin da ya hada da jiragen ruwan Italiya da dana Faransa an dauke su zuwa gabar ruwan Italiya.

Akalla mutane 1,700 ne suka rasu a bana a kokarin tsallaka Tekun Baharum.

Kungiyar Kula da Kauran Al'umma ta Duniya ta ce adadin na iya karuwa zuwa 30,000.

A watan da ya gabata shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai sun kira taron gaggawa domin tattauna matsalar bayan da mutane fiye da 800 suka rasu lokacin da jirginsu ya nutse.

Shugabannin sun amince su rubanya samar da kudi domin aikin ceto.

Karin bayani