Agaji ya kai inda barna ta fi yawa a Nepal

Sojojin Nepal na dora kayan agaji daga 'yan Indiya mazauna Sikkim a mota Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a sassauta ka'idojin kwastam da ke hana ruwa gudu

Ma'aikatan agaji a Nepal sun samu damar kaiwa yankunan da girgizar kasar makon jiya ta fi yin barna, inda hukumomi suka ce fiye da kashi casa'in cikin dari na gine-gine sun ruguje.

An ce babu komai sai baraguzai a wadansu garuruwa da kauyukan da ke tsaunukan da ke arewa da Kathmandu, babban birnin kasar, kuma masu aikin ceto sun ce ba sa sa ran samun mutanen da suka yi rai a karkashin baraguzan.

Yawan wadanda aka tabbatar sun rasa rayukansu ya haura dubu bakwai, kuma hukumomi sun ce mai yiwuwa adadin ya karu.

Ranar Asabar Majalisar Dinkin Duniya ta ce ka'idojin kwastam a filin jiragen sama na Kathmandu na yin tarnaki ga aikin rarraba kayan agaji.

Har yanzu dubban mutane na fatan samun agajin abinci, da magunguna, da tantuna.