An kashe 'yan sanda 17 a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mayakan Taliban na ci gaba da kai hare-hare a Afghanistan

Jami'an gwamnati a Afghanistan sun ce an kashe 'yan sanda 17 a wani hari da 'yan kungiyar Taliban suka kai a arewacin yankin Badakhshan.

Shugaban yankin Abdullah Naji, ya shaida wa manema labarai cewa an kai harin ne wajen da 'yan sanda suke bincikar ababen hawa da ke gundumar Wardoj a ranar Lahadi da daddare.

Mr Naji ya ce har yanzu ba a ga 'yan sanda 26 ba.

Harin na zuwa ne kusan makonni biyu bayan da mayakan Taliban suka kaddamar da hare-haren da suke kira na bazara a Afghanistan.