Agogon komai da ruwanka na Apple bai son jarfa

Hakkin mallakar hoto Michael Lovell
Image caption An daura agogon komai-da-ruwanka na Apple a hannu mai jarfa

Kamfanin kwamfuta na Apple ya ce akwai yiwuwar agogon komai-da-ruwanka da ya kera ya yi gardama idan aka daura shi a hannun da akayi wa jarfa (tatoo).

Kamfanin ya ce duhun launin zane zanen jarfar zai sa wasu na'urorin fahimtar yanayi na agogon su dimauce.

Sai dai kamfanin Apple ya ce ba agogon da ya kera ne kadai ke fuskantar matsala da jarfa a jikin fatar hannun ba.

"tawadar da ake zana jarfa da ita zata iya tare hasken da na'urorin fahimta na agogon zasu yi amfani da su''.

Mista Matt Siegel, ma'aikacin jarida a kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce agogon na Apple yana kullewa idan aka daura shi a hannu mai jarfa, kuma baya bayar da sautin nunawa mutun sabon sako ya shigo.

Wasu rahotanni daga masu amfani da agogon sun ce babbar fasaha ce aka yi amfani da ita wajen kera agogon, kuma agogon yana aiki da kyau idan ba a hannu mai jarfaba.

Sauran agogunan komai da ruwanka na wasu kamfanoni ma suna fuskantar irin wannan matsala idan aka daura su a hannaye masu jarfa.