An rada wa Gimbiyar Biritaniya suna Charlotte

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jaririyar gidan sarautar Ingila ta ci suna Gimbiya Charlotte

Fadar Sarauniyar Ingila ta ce Yarima da Gimbiyar Cambridge sun rada sunan 'yar da suka haifa a makon jiya, inda aka ba ta sunan Charlotte Elizabeth Diana.

Jaririyar -- wadda ita ce ta hudu a jerin wadanda za su yi sarautar Biritaniya -- za a dinga kiranta mai Girma Gimbiya Charlotte ta Cambridge.

A ranar haihuwar ta dai, an yi ta harba bindiga sama inda aka ji karar a baki dayan birnin London domin nuna farin ciki da karuwar da aka samu.