Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 02/05/2015

'Yan kabilar Mbum mazauna Adamawan Kamaru sun karbi bakuncin 'yan uwansu mazauna kasashen ketare a wurin bikin al'adarsu da kuma nuna wasannin gargajiya da ake kira "Mgbor Yanga".

Wannan ne dai karo na 913 da ake gudanar da wannan biki wanda aka fara a shekara ta 933 miladiyya, lokacin da aka kafa masarautar wannan kabila a Adamawan Kamaru.

'Yan kabilar dai sun yi amanna cewa kakanninsu sun kafa masarautar ce bayan tasowarsu daga kasar Yaman.

Wannan bikin kuma na ba wa Mbumawan damar ganawa da juna, su kuma tattauna batutuwan da suka shafi ci gabansu da kuma karfafa dankon zumunci.

Tun shekara ta 1997 ne dai, wannan bikin ke gudana a karkashin jagorancin Belaka Salihu Saw Mbum wanda shi ne sarkin kabilar na yanzu.

Mohaman Babalala ya aiko mana wannan rahoton daga Yaounde.