Sojin Nigeria sun fatattaki 'yan Boko Haram

Image caption Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da kai hare-hare ta sama da ta kasa kan mayakan kungiyar Boko Haram

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda dakarunta suka fatattaki mayakan Boko Haram lokacin da suke kai hare-haren sama da jiragen yaki a sansanin mayakan da ke dajin Sambisa.

A bidiyon -- wanda aka dauka daga cikin jirgi -- an nuna yadda matukan jirgin ke tarwatsa daruruwan mayakan inda suke ranta-a-na-kare suna bin mabanbantan hanyoyi.

Ana iya ganin yadda mayakan na Boko Haram ke gudu suna shiga manyan motoci da babura yayin da wasu ke gudun famfalaki.

Wannan ne dai karo na farko da sojin Najeriya suka saki bidiyo da ke nuna ayyukan da suke yi a dajin.