An karfafa dokar hana satar fasaha a Rasha

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Yadda ake satar fasahar wakoki ta intanet

Rasha tana kara tsaurara aiki da dokar yaki da satar fasahar mutane da intanet.

A cikin shekara ta 2013 ne aka bullo da dokar wacce ta bai wa hukumomi a kasar ikon umurtan kamfanonin intanet su yanke hanyoyin shiga shafukan da suke satar fasahar wasu.

Dokar daga farkon kafa ta ana aiki da ita ne a shafukan dake satar fasahar fina finai.

Yanzu da aka yi mata gyara, dokar zata rika aiki a shafukan da ke satar fasahar wakoki da litattafai da manhajojin kwamfuta.

Sai dai har yanzu dokar ba zata yi aiki a shafukan dake satar hotuna ba.