Buhari ya gana da gwamnonin APC

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Janar Buhari da mataimakinsa Farfesa Osinbajo

Shugaban Nigeria mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari, ya gana da gwamnonin jam'iyyar APC a Abuja babban birnin kasar.

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha bayan tattaunawar ya shaida wa manema labarai cewar manufar ziyarar ita ce su bayyanawa Janar Buhari matsalolin da wasu jihohin ke fuskanta.

Tun bayan da jam'iyyar APC ta lashe zaben shugaban kasa, shiyyoyin kasar daban-daban ke ta zawarcin neman a ba su wasu mukamai musamman na shugaban majalisar wakilai da kuma na dattawa.

Har yanzu uwar jam'iyyar APC ba ta bayyana rarraba mukaman siyasa ba, amma bayanai na nuna cewar an samu rarrabuwar kawuna tsakanin 'ya'yan jam'iyyar a kan yadda rabon zai kasance.

A ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Nigeria.